A jiya Jamu’a, wakilin CMG ya samu labari daga ofishi mai kula da aikin ceton mutane daga bala’in girgizar kasa da ya abku a gundumar Tingri karkashin birnin Shigatse na kasar Sin cewa, yanzu haka, an kafa gidajen wucin gadi 7733, da tantuna 9941, tare da tsugunar da mutane 47787 da bala’in girgizar kasa ya ritsa da su. Wadannan alkaluma sun nuna cewa, an riga an kammala aikin tsugunar da dukkan mutanen wurin bisa wani mataki na wucin gadi.
A ranar 7 ga watan Janairun da ya gabata ne dai, aka samu abkuwar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 6.8 a gudumar Tingri ta birnin Shigatse dake jihar Xizang ta Sin. Kana a halin yanzu, ban da mutanen da aka tsugunar da su cikin gidaje na wucin gadi da tantuna, ganin yadda bala’in girgizar kasa ya lalata gidajensu sosai, akwai wasu mutane 10772 da gidajensu ba su lalace sosai ba, wadanda aka yi bincike kan gidajensu, sa’an nan aka tabbatar da cewa za su iya ci gaba da rayuwa cikin tsoffin gidajensu, kuma babu bukatar tsugunar da su cikin gidajen wucin gadi ko tantuna. (Bello Wang)