An kammala bikin baje kolin fasahohin tattara manyan bayanai na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023 a birnin Guiyang, fadar mulkin lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an cimma manyan nasarori a yayin bikin na yini 3 wanda ya kammala a jiya Lahadi, inda aka sanya hannu kan takardun yarjeniyoyin zuba jari da darajar su ta kai kudin Sin yuan biliyan 61.3, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 8.7.
A baje kolin na bana, an baje sama da sabbin fannonin kasuwanci masu nasaba da bangarori har 220, inda aka baje kolin sama da sabbin kayayyaki 900, da fasahohi da manhajoji da dama, matakin da ya janyo mahalarta sama da 180,000, kamar dai yadda mashirya bikin suka bayyana.
Tun da fari, an gayyaci sama da baki 338 daga kasashen waje, da hukumomin kasa da kasa 50. Kuma bikin ya hallara sanannun kamfanoni kasa da kasa 83.
Bikin wanda aka kira “Babban dandalin tattara manyan bayanai na Sin” ya gudana ne a lardin Guizhou mai tsaununa, wanda ke zama cibiyar farko da aka ayyana, a matsayin cikakken yankin gwaji a fannin tattara manyan bayanai. Kuma lardin ya samu kyautatuwar zamantakewa da tattalin arziki, sakamakon gajiyar da ya ci daga fannin. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)