An kammala gasar “Gadar Sinanci” ta daliban jami’o’in kasar Masar karo na 22, a jami’ar Suez Canal dake lardin Ismailia na arewacin kasar.
Gasar wadda ofishin jakadancin Sin dake Masar, da cibiyar Confucius ta jami’ar Suez Canal suka dauki nauyin gudanarwa, ta kunshi sassa 3, da suka hada da gabatar da jawabi, da wasan nuna fasaha, da kuma kacici-kacici.
Bayan kammala gasar ta wannan karo a jiya Litinin, ‘yan takara 3 da suka yi fice cikin mutane 12 da suka kai zangon karshe daga jami’o’i 6, sun karbi manyan kyaututtuka.
Da yake tsokaci game da nasarar da ya samu, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ‘dan takarar da ya zo na daya Loay Adel Mohamed, wanda ke karatu a jami’ar birnin Alkahira, ya bayyana farin cikin sa, da matakan da ya bi wajen koyon Sinanci, da ma yadda ya nuna fasahar wasan kwaikwayo ta “canza kama”, daga wasan kwaikwayon lardin Sichuan ko wasan “bian lian”, wanda ya yi matukar kayatar da ‘yan kallo.
A cewar sa, “Babban abun alfahari ne lashe wannan gasa a yau, saboda a yanzu na samu damar fafatawa a gasar da za a yi a kasar Sin, inda zan nuna kaunata ga al’adun kasar Sin”.
A nasa tsokaci kuwa, jakadan Sin a Masar Liao Liqiang, ya ce a halin da ake ciki, al’ummun Sin da na Masar na aiki tukuru, domin cimma nasarar manyan burikan su. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)