Kamfanin gine gine na kasar CCECC, ya kammala kashi na farko na layin dogo, wanda jiragen kasa masu amfani da lantarki za su yi zirga zirga a kan sa, a jihar Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya.
A jiya Laraba ne dai kamfanin ya kammala sashen farko na aiki mai tsawon kilomita 13, cikin jimillar layin dogo mai tsawon kilomita 27, bayan fara aikin a shekarar 2010.
Gwamnatin Lagos ta yiwa aikin lakabi da “Lagos Rail Mass Transit” ko (LRMT) a takaice. Kuma a sashen farkon da aka kammala, layin dogon ya ratsa unguwar Okokomaiko mai yawan al’umma dake yammacin birnin, zuwa unguwar Marina mai yawan hada-hadar kasuwanci dake tsibirin jihar ta Lagos.
Aikin dai wani muhimmin jigo ne cikin manufofin gwamnatin jihar Lagos, dake da nufin biyan bukatun kasuwanci da harkokin raya tattalin arzikin jihar, wadda ke cikin manyan biranen kasuwanci na duniya mafiya saurin bunkasa.
Da yake kaddamar da aikin, gwamnan jihar Lagos Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya bayyana shi a matsayin muhimmin al’amari mai cike da tarihi. Gwamna Sanwo-Olu ya kara da cewa, jihar Lagos ta zama jiha ta farko daya tilo a dukkanin yankin yammacin Afirka, da ta yi nasarar samar da kudaden gudanar da aikin gina layin dogo na kashin kan ta daga lalitar gwamnati. (Saminu Alhassan)