A yau Lahadi, babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kammala rahaza karo na 3 na shagalin murnar bikin bazara na kasar Sin na shekarar 2024. An ce wannan shagali ya shafi al’adun gargajiyar kasar, kuma ya nuna yadda Sinawa suke kokarin neman samun zaman rayuwa mai inganci, da karfin zuci da suke da shi wajen ganin hakan ya tabbata. Kana da wannan shagalin bikin ne za a mika fatan alheri na sabuwar shekara ga daukacin Sinawa da suke zama a wurare daban daban na duniya. Za a nuna wannan shagalin a kafofi daban daban na CMG a daren ranar 9 ga watan Fabrairu, bisa agogon kasar Sin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp