An karrama dan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal a wani babban taron masana tattalin arziki na duniya a yankin Glasgow da ke Birtaniya.
Taron wanda aka gabatar da shi ranar Alhamis 30 ga Yulin 2022 a Birtaniya, wanda aka karrama, Dauda Lawal, É—an takarar gwamnan Jihar Zamfara a Æ™arkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaÉ“en 2023, kuma tsohon babban daraktan ‘First Bank’ ya amshi lambar girmamawa tare da gabatar da jawabi a taron masanan mai taken ‘The 2022 Reputable Banks and Fintech Awards/Conference (RBFA)’.
Baya ga mashahuren masana tattalin arziki da suka halarci taron daga sassan duniya, manyan bankuna da kamfanonin inshora da masu zuba hannun jari duk suna cikin mahalarta taron.
Masu fashin baƙi kan harkokin yau da kullum sun ambaci taron na wannan shekara a matsayin ɗaya daga cikin wadanda suka fi armashi a tsawon shekarun da aka kwashe ana gabatarwa.
Yayin da yake gabatar da jawabinsa, Dauda Lawal ya maida hankali wurin jawo hankalin masana tattalin arziki da su waiwaiyi Afirka da irin tarin albarkatun da take da su, musamman ma Nijeriya.
A cewarsa, lamari ne da ke buƙatar masu zuba hannun jari su shigo domin raya tattalin ƙasashen Afirka.
A ƙarshe an gabatar da shaidar girmamawa ga Dakta Dauda Lawal, a matsayin sanannen masanin a fannin tattalin arziki da ke bada gudummawa ga wannan fanni a fadin duniya.