Akalla mutum 16 ne aka ruwaito cewar sun mutu bayan kwashe tsawon kwanaki uku ana gwabza artabu tsakanin kungiyoyin asiri kan kula da wuraren ajiye kananan motocin bas a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Rikicin ya fara tashi ne a yankin Idu da ke karamar hukumar Uruan yayin da ya fantsama zuwa wasu yankunan Use Offot, Ekpri Nsukara, da yankin Oniong dukka da suke karamar hukumar Uyo, rikicin ya janyo mutuwar mutum 16 da lalata miliyoyin kaddarori.
- Shugaban PDP Na Shiyyar Kudu Maso Yamma, Adagunodo, Ya Rasu Yana Da Shekaru 62
- FAAN Ta Bai Wa Kamfanonin Jirage Umarnin Kwashe Jiragensu Daga Filin Jirgin Saman Abuja
Wani dan jarida a yankin, Nora Iwang da Aniefiok Usen, dukkaninsu mazauna yankin Nwanibba sun bayyana yadda rikicin ya janyo tashin hankali da firgici ga al’ummar yankin.
Mutum takwas an yi musu yankan rago ne a Use Offot da kuma wasu sama da goma da aka kashe a Anua, Ekpri Nsukara da kauyen Oniong yayin da wasu da dama suke kwance a asibitoci daban-daban domin jinyar raunukan da aka musu.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Odiko Macdon, ya tabbatar da kisan, amma ya ce, mutum hudu ne kawai aka kashe, ya bada tabbacin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Olatoye Durosinmi, ya umarci a dauki matakan da suka dace wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin biyu da shawo kan dukkanin wasu baraka.
“Kwamishinan ya yi tir da wannan lamarin kuma ya tabbatar da cewa sai an kamo masu hannu a wannan mummunar ta’asar domin su fuskanci hukunci.”
Kwamishinan ya umarci jama’a da su cigaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai tare da cigaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da biyayya wa doka da oda.