Sojojin kasar Chadi sun kashe ‘yan Boko Haram da dama a kofar gidan shugaban kasar da ke Ndjamena na kasar Chadi a lokacin da ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kai hari a daren Laraba a fadar shugaban kasar.
Majiya mai tushe ta ce an kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan yayin da aka kama wasu da ransu.
- Tinubu Ya bayar Da Umarnin Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai Wa Sansanin Sojoji A Borno
- Gwamna Yusuf Zai Raba Naira Biliyan 3 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kano
A halin da ake ciki, gwamnatin kasar Chadi ta bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankula bayan yunkurin kai hari a fadar shugaban kasar da ke Ndjamena.
Ministan tsaron kasar Abderamane Koullamallah, wanda kuma shi ne mai magana da yawun gwamnatin Chadi, ya tabbatar wa daukacin kasar cewa gwamnati ta shawo kan lamarin a halin yanzu.
Ministan ya bayyana haka ne jim kadan bayan jami’an tsaron Chadi sun dakile harin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai musu.