Mataimakin ministan ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin Sheng Qiuping, ya ce an kusa kammala shirye-shiryen gudanar da baje kolin kasa da kasa na hajojin shige da fice na kasar Sin ko CIIE karo na takwas, wanda zai gudana tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba mai zuwa a birnin Shanghai.
Yayin gudanarsa, masu baje hajoji 4,108 daga kasashe, da yankuna da hukumomin kasa da kasa 155 za su hallara. An kuma tanaji wurin baje hajoji da fadinsa ya haura sakwaya mita 430,000, fadin wurin da ya kafa sabon tarihi a baje kolin.
Sheng Qiuping, ya ce a bana baje kolin na CIIE ya tanaji karin fadin yankin musamman domin baje hajojin nahiyar Afirka, inda ake sa ran adadin kamfanonin nahiyar masu halartar baje kolin zai karu da kaso 80 bisa dari a mizanin shekara-shekara. (Saminu Alhassan)














