Wasu da ba a san ko suwaye ba sun yi wa fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya dukan tsiya a yammacin yau a Kano.
A hotunan matashiyar da suka bayyana a shafukan sada zumunta da har Leadership Hausa ta samu gani bata-garin sun canza mata kama da raunuka a fuskarta.
- Kotu Ta Yanke Wa Murja Hukuncin Sharar Asibiti A Kano
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Aike Da Murja Kunya Zuwa Gidan YariÂ
Tuni dai aka fara yin kira ga jami’an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar zakulo wadanda suka yi mata wannan aika-aika.
Murja Ibrahim Kunya dai tayi kaurin suna a shafin TikTok inda take da mabiya masu dimbin yawa,dake bibiyar shafin nata.
Kuma yar gwagwarmayar siyasa ce da take goyon bayan Gwamnan jahar Kano Eng Abba Kabir Yusuf.