Tun daga ranar 30 zuwa 31 ga watan Oktoba, Sin ta gudanar da taro game da harkokin kudi na kwamitin kolin JKS karo na farko a birnin Beijing, inda sakatare janar na kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ya nazarci ayyukan harkokin kudi da aka gudanar a cikin shekaru 10 da suka gabata, da tsara ayyuka masu ruwa da tsaki da za a yi yanzu da kuma nan gaba.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata harkokin kudi su samar da hidima mai inganci wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Ya kuma bukaci a inganta samar da hidimar kudi kan manyan tsare-tsare da manyan fannoni, da kuma fannonin dake fuskantar kalubale. Haka kuma a kara amfani da albarkatun kudi wajen sa kaimi ga yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kera kayayyaki na zamani, da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da taimakawa kanana da matsakaitan kamfanonin, da nuna goyon baya ga aiwatar da manufofin samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, da raya yankuna daban daban, da tabbatar da wadatar hatsi da makamashi, da raya tsarin hukumomin hada-hadar kudi da kasuwanni, da bude hanyoyin shigar da jari zuwa ga cibiyoyin raya tattalin arziki da sauransu. (Zainab)