Jihar Indiana da ke Amurka ta maka mahukuntan kamfanin ByteDance wanda ya mallaki manhajar TikTok a kotu kan zargin nuna wa yara abubuwan bata tarbiyya.
Karar tana tuhumar manhajar TikTok da saba dokokin kare masu mu’amala da shi.
Babban mai shari’a na jihar Todd Rokita ya kuma zargi TikTok da kin bayyana yiwuwar cewa kasar China za ta iya tatsar bayanai ta manhajar. Inda ya bayyana manhajar a matsayin ‘kura a cikin fatar akuya.’
Ƙarar ta ce tsarin na TikTok na tura wa yara bidiyon da ya kunshi shan kayan maye, da tsiraici, da lalata da kuma munanan kalamai.
BBC Hausa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp