Yayin karatowar bikin bazara na shekarar Loong bisa al’adar gargajiyar kasar Sin, an gudanar da jerin bukukuwan murnar bikin a Dubai na hadaddiyar daular Larabawa. Inda a kan alluna iri iri fiye da 230 na filin jiragen sama na kasa da kasa na Dubai, da kantuna mara harajin kwastan, da manyan yankunan kasuwanci, da babban dakin wasan kwaikwayo na Dubai da dai sauransu, an nuna dandanon shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, wanda ya jawo hankalin mazauna wurin masu dimbin yawa.
A ranar 7 ga wata bisa agogon wurin, a filin jiragen sama na kasa da kasa mafi zirga-zirga a duniya, wato filin jiragen sama na Dubai, an gudanar da bukukuwan murnar bikin bazara na Sin, inda aka nuna dandanon shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG, wanda ya kasance wani mataki da aka dauka shekaru 5 a jere. Kana a yau, wato jajibirin bikin bazara, allo mafi girma a filin jiragen saman zai watsa shirye-shiryen bikin sabuwar shekara kai tsaye.
A shekarar 2022, yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta filin jiragen sama na kasa da kasa na Dubai ya zarce miliyan 66.09, wanda ya kai matsayi na farko a duniya, da baiwa filin jirgin saman damar kiyaye wannan matsayi wasu shekaru 8 a jere. An yi hasahen cewa, a lokacin bikin bazara, fasijojin kasar Sin masu yawa za su ziyarci Dubai ko canja jirgi a can. Inda wasu daga cikin fasinjoji Sinawa suka bayyana cewa, suna jin dadin kallon bidiyon dandanon shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa a ketare, wanda ya samar da wani yanayi mai annashuwa na murnar bikin.(Safiyah Ma)