A ranar 17 ga watan Fabrairu, agogon birnin New York ne, aka yi wani zama na musamman na nuna fim din Nezha 2 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kungiyar masu sha’awar karanta littattafai na kasar Sin dake MDD suka dauki nauyin shiryawa tare. Fiye da baki 150 da suka hada da mataimakin babban sakataren MDD Xu Haoliang, da jami’an diflomasiyyar kasashen Faransa, Rasha, Girka, Thailand da sauran kasashe a MDD, da ma’aikatan hedikwatar MDD, da ’yan jarida sun halarci bikin nuna fim din.
Xu Haoliang, mataimakin babban sakataren MDD ya bayyana cewa, sakin fim din Nezha 2 a kasashe da yankuna da dama na duniya ya sa kaimi ga mu’amala tsakanin jama’a da al’adu tsakanin kasar Sin da sauran kasashe. Fim din ya hada kasashe da al’adu daban-daban ta hanyar ba da tatsuniyoyi da labaru a cikin al’adun gargajiya na kasar Sin, wanda ya kara samun fahimtar juna tsakanin al’umma. Yadda aka shirya fim din Nezha 2 ya kuma nuna cewa, bunkasuwar fasahar shirya fina-finan cartoon ta kasar Sin ta kai matsayi na duniya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp