A jiya Alhamis ne aka sanya hannu kan takardun hadin gwiwa, da ayyukan raya tattalin arziki da cinikayya 14, tsakanin Sin da wasu kasashen Afirka da dama, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 170.
An sanya hannu kan wadannan takardu ne a jiya Alhamis, yayin taron bunkasa tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka, wanda ya gudana a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
Yarjejeniyoyin dai sun kunshi bangarorin hadin gwiwar yankuna, da muhimman tsare-tsaren ayyuka, da samar da kudaden gudanarwa, da fannin hadin gwiwar zuba jari da cinikayya.
Kaza lika, a yayin taron, sassan dake lura da cinikayya na lardunan kasar Sin 6, su ma sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya da wasu kasashen Afirka.
Taron dai ya samu halartar jakadu 29 daga kasashen Afirka 15, da suka hada da na Aljeriya, da Habasha, da Angola, da Ghana, da Kenya.
Bugu da kari, mahalartansa sun yi amfani da dandalin taron, wajen yayata manufar yankin gwaji na zurfafa hadin gwiwar raya tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka kafa. (Mai Fassarawa: Saminu Hassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp