An rufe bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya wato CISCE karo na uku na tsawon kwanaki 5 a yau, kuma daga bisani an gudanar da taron manema labaru game da bikin a yammacin yau, inda kungiyar sa kaimi ga yin ciniki ta kasar Sin ta gabatar da cewa, yawan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da aka daddale da abubuwan neman hadin gwiwa a gun bikin ya zarce dubu 6.
A yayin gudanar da bikin karo na uku, yawan kamfanonin kasashen waje da suka halarci bikin ya ci gaba da samun karuwa, wato daga kashi 26 cikin dari a karo na farko, da kashi 32 cikin dari a karo na biyu, zuwa kashi 35 cikin dari a karo na uku. A cikin wannan kaso, yawan manyan kamfanonin duniya 500 wadanda suke gaba da manyan kamfanonin sana’o’i daban daban a duniya da suka halarta ya zarce kashi 65 cikin dari, kana kamfanonin da suka halarci bikin sun fito ne daga kasashe da yankuna 75 a wannan karo, kana kamfanonin Amurka da kasashen kungiyar EU da kasar Japan duk su ma sun halarci bikin.
Mataimakin shugaban kungiyar sa kaimi ga yin ciniki ta kasar Sin Li Xingqian ya yi bayanin cewa, bikin CISCE ya shaida karfin kasar Sin na samar da kayayyaki da kera kayayyaki da kuma yin kirkire-kirkire. Kasar Sin ta kasance a muhimmin matsayi a duniya ta fannin samar da kayayyaki, kuma ya kamata a yi hadin gwiwa tare da ita da kuma yin hadin gwiwa tare da duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp