Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron.
A gun bikin rufe taron, an zartas da kudurin rahoton aikin kwamitin dindindin na taron, da rahoton da kwamiti mai kula da kudurori ya gabatar game da bincike kan kudurorin da aka gabatarwa taron, kana da kudurin siyasa na taron da dai sauran muhimman takardu. (Amina Xu)














