A jiya Asabar ne aka kammala taron kolin G77, wato rukunin kasashe 77 da kasar Sin a hukumance, inda wakilai mahalarta taron suka fitar da sanarwar Havana.
Yayin taron kolin da aka gudanar, wakilai sun jinjinawa shawarar raya dukkanin duniya da kasar Sin ta gabatar, kuma sun nuna goyon baya ga hadin gwiwar tattalin arzikin zamani, da ta kimiyya da fasaha tsakanin kasashen 77 da kasar Sin, ta yadda za a ingiza ci gaban kasashe masu tasowa lami lafiya.
Shugaban kungiyar AU na wannan karo, kuma shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, ya yi tsokaci da cewa, “Muna ganin cewa, shawarar hadin gwiwar tattalin arzikin zamani da kasar Sin ta gabatar, za ta sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma wannan kaso ne daga cikin babbar shawarar ziri daya da hanya daya”.
A nasa bangare, firaministan kasar Jibouti Abdoulkader Kamil Mohamed, ya ce “Hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, muhimmiyar hanya ce da za ta ingiza hada kan kasa da kasa, don haka muna matukar maraba da shawarar raya dukkanin duniya da kasar Sin ta gabatar, kuma ya dace mu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu”. (Mai fassara: Jamila)