A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo”, inda wakilai fiye da 1600 daga kasashe da yankuna fiye da 130 suka halarci taron da tattauna taswirar kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa.
Babban sakataren taron Ren Xianliang ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an zartas da rahoton aiki na taron yanar gizo na duniya na shekarar 2025 a gun taron koli a wannan karo, da amincewa da kafa kwamitin kula da kiyaye abubuwan al’adu ta yanar gizo, da kwamitin kula da harkokin ciniki ta yanar gizo, da gudanar da taron tattaunawa kan cika shekaru 10 da gabatar da ra’ayin kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo, inda mahalartar taron tattaunawar suka nunar da cewa, an zurfafa ra’ayin a fadin duniya a shekaru 10 da suka gabata, kuma an samu jerin nasarori wajen sarrafa harkokin raya ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya. (Zainab Zhang)














