An rufe taron ministoci karo na 13 na kungiyar WTO, a birnin Abu Dhabi fadar mulkin hadaddiyar daular Larabawa a Asabar din nan. Yayin taron manema labarai da aka gudanar bayan taron, shugaban taro na wannan karo, kana karamin ministan cinikayyar shige da fice na hadaddiyar daular Larabawa Thani Al Zeyoudi, da babbar daraktar WTO Ngozi Okonjo-Iweala, sun amsa tambayoyin da aka yi musu, inda suka jinjinawa rawar ganin da Sin take takawa, wajen kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban.
A bangarensa Thani Al Zeyoudi, ya ce Sin ta nuna himma da gwazo wajen shiga tarukan WTO, da ba da gudunmawa yadda ya kamata, don ingiza shawarwari, da sulhu da aka gudanar. Ya ce yawan cinikin da Sin take gudanarwa a duniya na bayyana alkawarin da take yi wajen kiyaye manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban.
A nata bangare kuwa, Ngozi Okonjo-Iweala ta yi nuni da cewa, Sin ta taka rawar gani wajen shiga ajandar taron, wanda hakan ya bayyana goyon bayan da take baiwa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. (Amina Xu)