A jiya Alhamis 27 ga watan nan ne aka rufe zama karo na hudu, na taron dandalin bayanai na Data na kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya ko UNWDF a takaice, a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, inda aka fitar da Sanarwar Hangzhou, mai kunshe da muhimman sakamakon da aka samu a yayin taron.
Manufar Sanarwar Hangzhou, ita ce tafiyar da harkokin da ke da nasaba da bayana na Data yadda ya kamata, a kokarin kara azama ga aiwatar da ajandar neman samun dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2023. Sanarwar ta kuma nuna cewa, bayanan Data mai inganci dake samun karbuwa daga kowa da kowa, wadanda ake bayarwa a kan lokaci ba tare da rufa-rufa ba, wani muhimmin bangare ne na gaggauta cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa, da tinkarar matsaloli daban daban yadda ya kamata. (Kande Gao)