An yi garkuwa da jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da shugaban tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Maradun jihar Zamfara.
Maradun ta kasance mahaifar gwamna mai mulki, Bello Mohammed Matawalle wanda kuma shine dan takara a jam’iyyar APC da ke neman yin tazarce.
An sace sune akan hanyarsu ta zuwa Hedikwatar hukumar zabe inda ake tattara sakamakon zabe a garin Gusau bayan dauko sakamakon zaben karamar hukumar Maradun.
Kakakin hukumar INEC, Muktari Janyau ya tabbatar da sace jami’an, inda ya ce sun shigar da korafi ga ‘yansandan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp