A yammacin yau Litinin ne aka gudanar da bikin sake bude ofishin jakadancin kasar Sin a Nauru a wani otel dake kudu maso gabashin kasar dake tsibirin Pasifik.
Ministan harkokin waje da cinikayya na Nauru Lionel Aingimea da Luo Zhaohui, shugaban hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, wanda ya halarci bikin a matsayin wakilin gwamnatin kasar Sin, sun kaddamar da allon ofishin jakadancin kasar Sin.
- Bankunan Kasashen Ketare Sun Yaba Da Bunkasuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin
- Ministan Harkokin Wajen Nauru: Dawo Da Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Nauru Muhimmin Lokaci Ne A Tarihi
Kafin wannan tawagar jami’an diplomasiyya ta kasar Sin, ta yi bikin daga tutar kasar Sin a Nauru, karon farko cikin kusan shekaru 19 da aka daga jar tutar mai taurari 5 a tsibirin dake yankin Pasifik.
Bugu da kari, a yau Litinin, tawagar jami’an diplomasiyya ta kasar Sin ta yi bikin daga tutar kasar Sin a Nauru, karon farko cikin kusan shekaru 19 da aka daga jar tutar mai taurari 5 a tsibirin dake yankin Pasifik.
Jami’an da aka dorawa alhakin farfado da ofishin jakadancin Sin a Nauru ne suka gudanar da bikin a harabar dake dauke da ofisoshinsu na wucin gadi.
Shugaban tawagar jami’an diplomasiyya na kasar Sin Wang Xuguang, ya shaidawa manema labarai cewa, dangantakar kasashen Sin da Nauru na dauke da dimbin damarmaki.
A ranar 15 ga watan Junairu ne gwamnatin kasar Nauru ta sanar da cewa, ta amince da manufar Sin daya tak a duniya, kana ta katse hulda da hukumomin yankin Taiwan, haka kuma ta shirya dawo da huldar diplomaisyya da kasar Sin.
A kuma ranar 24 ga wata ne a nan birnin Beijing, kasashen Sin da Nauru suka rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwa, wadda ta sanar da dawo da huldar diplomasiyya a tsakaninsu. (Masu fassarawa: Muhammed Yahaya, Fa’iza Mustapha)