A ranar Litinin aka bayyana Gwamna Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Jami’in zaben gwamnan jihar, Farfesa Tanko Ishaya, ya bayyana cewa Sule na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 347,209 inda ya doke abokin takararsa David Ombugadu na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 283,016.
Sai dai PDP ta nuna rashin gamsuwarta da sakamakon inda ta ce za ta nemi a hakkinta a kotu, yayin da APC ta ce za ta kuma kalubalanci kananan hukumomin da PDP ta lashe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp