Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da alkaluma dake cewa, a shekarar 2024, adadin shige da ficen jama’a a kasar Sin ya kai miliyan 610, adadin da ya karu da kashi 43.9% kan makamancin lokaci na shekarar 2023, ciki har da baki kimanin miliyan 65 da suka shigo kasar, wanda ya karu da kashi 82.9%. Kuma yawan baki da suka shigo kasar Sin ba tare da bukatar neman biza ba ya kai miliyan 20, adadin da ya karu da kashi 112.3% kan makamancin lokaci na shekarar 2023.
A yau Talata, hukumar shige da fice ta kasar Sin ta fitar da alkaluma kan ayyukanta na shekarar bara, inda ta ce adadin biza da ta bayar ga baki ta kai kimanin miliyan 2.6, adadin da shi ma ya karu da kashi 52.3% bisa na makamacin lokaci na shekarar 2023. Yayin da ta kuma ta samarwa baki dubu 72, hidimar tsawaita wa’adin biza. An ce, yawan mutane da manufar “ba da izinin shiga kasar Sin ba tare da bukatar biza ba” ya amfana, ya karu da kashi 113.5% bisa na shekarar 2023. (Amina Xu)