Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata, shirin da shugaba Xi Jinping ya gabatar na gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, ya samu sakamako mai kyau. Kuma har kullum, kasar Sin na kasancewa amintacciyar abokiya ta kasashen Latin Amurka da Caribbean.
Lin Jian, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum, wanda ya gudana a yau Talata, lokacin da wani dan jarida ya yi tambaya game da sakamakon ci gaba da aka samu, don gane da manufar gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean.
- Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Na Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwa
- Da Dumi-Dumi: Wani Abu Ya Fashe A Kasuwa, Mutane Sun Raunata A Jos
Game da kama aikin Navinchandra Ramgoolam a matsayin firaministan sabuwar gwamnatin kasar Mauritius kuwa, Lin Jian ya ce, kasar Sin ta lura da rahotanni masu nasaba da hakan, kuma ta taya Ramgoolam murnar zaben da aka yi masa a matsayin firaministan Mauritius.
Kazalika kasar Sin tana fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnatin Mauritius, don yin amfani da damar aiwatar da sakamakon da aka cimma, a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka yi a birnin Beijing, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Mauritius.
Lin Jian ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kungiyar APEC na bana, zai kuma yi bayani kan manufofin kasar Sin, na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da na yankin tekun Pasifik. (Safiyah Ma)