An sanya kaburburan sarakunan daular Xixia ta kasar Sin cikin jerin muhimman wuraren tarihi na duniya, yayin taro na 47 na kwamitin kula da kayayyakin gado na tarihi na duniya, karkashin laimar kungiyar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) , da ya gudana a birnin Paris na kasar Faransa, jiya Juma’a.
Da wannan kari, adadin muhimman wuraren tarihi na duniya a kasar Sin ya kai 60.
Kaburburan sarakunan daular Xixia sun kunshi dimbin tsoffin gine-gine na lokacin daular Xixia ta kasar Sin, wadda ta kasance tsakanin shekarar 1038 zuwa ta 1227, da mutanen tsohuwar kabilar Tangut suka kafa a arewa maso yammacin kasar Sin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp