Rundunar ƴansanda ta Jihar Borno, ta fara bincike kan wani rahoto da ya karaɗe kafafen sada zumunta, da ke cewa wata matashiya ta kashe kanta bayan an tilasta mata aure a ƙaramar hukumar Gubio ta jihar.
Rahoton ya bayyana cewa matar ta yanke shawarar kashe kanta ne bayan mahaifinta ya tilasta mata ta auri abokinsa.
- Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansanda na jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a Maiduguri, ya ce kwamishinan ƴansandan jihar CP Naziru Abdulmajid, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don gano gaskiyar abin da ya faru.
ASP Daso, ya ce rundunar ta kuɗuri aniyar gano haƙiƙanin gaskiya, tare da kira ga jama’a da ke da sahihan bayanai su fito su taimaka wajen binciken da ake yi.
Ya kuma shawarci jama’a da su yi hattara tare da kauce wa yaɗa labarai marasa tushe, musamman kan batutuwa masu sarƙaƙiya da ka iya tayar da hankali ko kawo rudani, yana mai tunatar da cewa hakan babban laifi ne a ƙarƙashin dokar laifukan yanar gizo ta shekarar 2015.
Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce da fushin jama’a a faɗin jihar, inda al’umma da masu fafutuka ke kira da a bincika tare da ɗaukan mataki cikin gaggawa don hana faruwar irin haka nan gaba.