Yau Asabar, a gun taron kayayyakin tarihi na UNESCO karo na 46 da aka gudanar a birnin New Delhi, babban birnin kasar Indiya, an shigar da “Layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing wato tsarin babban birni mafi kyau na kasar Sin” da Sin ta gabatar a hukumance a cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya. Kawo yanzu, yawan kayayyakin tarihi na duniya da Sin take da su ya kai 59.
Layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing yana cibiyar tsohon garin Beijing, wanda tsawonsa ya kai kilomita 7.8, an fara gina layin ne a karni na 13, wanda ya tsara tsoffin gine-gine da wadanda suka ruguje bisa tsari na tsohon birnin, kuma ya kunshi jimillar abubuwan gargajiya guda 15. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp