Hukumar kididdiga ta Kasa, ta bayyana yadda ‘yan kasuwa a Nijeriya suka shigo da madara ta kimanin naira biliyan 27, 664.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS na cewa an shigar da madarar ne daga kasashe hudu, inji BBC Hausa.
‘yan kasuwar sun yi amfani da damar ne, sa’ilin da ake rade-radin cewa, gwamnatin kasar za ta dakatar da shigo wa da madara daga Kasashen Ketare.
Gwamnati ta so ta haramta shigo wa da madarar ne sakamakon kayayyakin samar da madarar da gwamnatin ta ce ta samar a kwanakin baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp