Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, an tsara harba na’urar Chang’e-6 ta kasar Sin mai binciken duniyar wata, a rabin farko na bana.
A cewar hukumar, tuni aka kai kayayyakin na’urar Chang’e-6 zuwa cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin. Kuma za a gudanar da gwaje-gwaje kafin harba na’urar kamar yadda aka tsara.
Ta kara da cewa, yanzu haka, kayayyaki a cibiyar harba kumbunan suna cikin yanayi mai kyau, kuma tuni shirye-shiryen harba na’urar suka kankama. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp