Bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, don halartar taron koli na farko, na Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko GCC, tare da kai ziyartar aiki a kasar, an wallafa bayanin da Xi ya rubuta a jairdar Riyadh, mai taken “Yaukaka dankon zumunta, samar da makoma mai haske”.
Bayanin ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, alakar Sin da Saudiyya na bunkasa yadda ya kamata. Kasar Sin za ta yi amfani da wannan dama, don karfafa dangantakar abuta tare da Saudiyya bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da kara hadin-gwiwa don nuna adawa da shisshigin da sauran kasashe ke yi, da neman ci gaba cikin ‘yanci.
Kana, kasashen biyu za su yi kokari tare, don hade shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da “muradun samar da ci gaba na Saudiyya zuwa shekara ta 2030”. Bugu da kari, kasashen biyu, za su fadada mu’amala da juna a fannonin da suka shafi harkokin Majalisar Dinkin Duniya, da kasashen G20 da kungiyar hadin-kan Shanghai wato SCO da sauransu, a wani mataki na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, da samar da ci gaba a duk fadin duniya baki daya.
Bayanin Xi ya kuma ce, Sin babbar kasa ce dake kokarin shimfida zaman lafiya da ci gaba a duniya, da kara samar da sabbin damammaki ga kasa da kasa, ciki har da na Larabawa, don yaukaka dankon zumunta, da samar da makoma mai haske tare da ‘yan uwa kasashen Larabawa.
Bugu da kari, kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da amsar sako ga wakilan masu sha’awar koyon Sinanci na kasar Saudiyya, inda ya karfafa zukatan matasan Saudiyya, domin su yi kokarin koyon Sinanci, ta yadda za su taimaka wajen zurfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Saudiyya, da ma tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.
A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, koyon harsuna na sauran kasashe, zai ingiza zumuncin dake tsakanin al’ummomin kasashen, da taka rawa kan gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.
A kwanakin da suka gabata ne, matasan Saudiyya masu sha’awar koyon Sinanci sama da 100, suka aike da wasiku ga shugaba Xi domin shaida masa sakamakon da suka samu yayin da suke koyon Sinanci, inda suka bayyana cewa, suna son kara fahimtar kasar Sin, tare kuma da zurfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Saudiyya.
A halin da ake ciki yanzu, an riga an shigar da darasin Sinanci cikin manhajan ba da ilmi na Saudiyya, haka kuma an kafa sana’ar ilmi dake da nasaba da Sinanci a jami’ai 9 a kasar. (Mai fassarawa: Murtala Zhang, Jamila daga CMG Hausa)