Kwanan nan, aka wallafa littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1 a kasar Sin, wanda kwalejin nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin JKS ya tace.
Littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1, ya kunshi muhimman ayyuka kuma na asali na rubutun Xi Jinping kan raya tattalin arziki daga watan Nuwamban 2012 zuwa Disamban 2024. An tsara shi bisa tsarin lokaci, kuma ya kunshi rubuce rubuce guda 74 da suka hada da rahotanni, jawabai, laccoci, umarni da sauransu.(Safiyah Ma)