An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi.
Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha)