Albarkacin halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karo na 2, wanda ke gudana a birnin Astana na Kazakhstan, an gudanar da bikin kaddamar da shirin “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harsunan ketare, wanda kafar CMG ta gabatar a jiya Litinin a cibiyar shugaban kasar Kazakhstan.
Daga baya kuma manyan kafofin yada labarai fiye da 10 na wadannan kasashe 5, ciki har da gidan talibijin na hanyar siliki na Kazakhstan za su watsa wannan nagartaccen shiri.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi a gun bikin, inda ya ce shugaba Xi na dora babban muhimmanci kan huldar kasarsa da kasashen tskiyar Asiya, yana mai cewa, Sin ta nacewa matsayin sahihiyar kawa kuma makwabciya ga kasashen shiyya ba tare da tangarda ba.
Shirin da CMG ta gabatar, ya zamo ainihin mataki da Sin ta dauka na zurfafa zumuncin al’ummun bangarorin biyu, da kara zurfafa mu’amalar al’adunsu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp