Lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Malaysia, an yi bikin kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata masu jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay da rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, watau CMG ya samar, a jiya Talata a Kuala Lumpur fadar mulkin kasar.
Mataimakin firaminista na farko na kasar, Ahmad Zahid bin Hamidi ya aike da sakon taya murnar kaddamar da wannan shirin bidiyo. Baki fiye da 200 da suka fito daga bangaren siyasa da tattalin arziki da al’adu da kafofi yada labarai sun halarci bikin.
A cikin sakonsa, Zahid ya yi maraba da zuwan shugaba Xi Jinping, inda ya ce, shirin da CMG ta gabatar wani tubali ne mai muhimmanci dake shaida yadda kasashen biyu ke dada zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren al’adu da aikin yada labarai.
Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp