Wata kotun sojin Nijeriya ta musamman da ke zamanta a Maiduguri a jihar Borno ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin daurin rai-da-rai, yayin da wani daya kuma aka yi masa hukuncin daurin shekaru 15 bisa samun su da laifin safarar makamai ba bisa ka’ida ba ga ‘yan ta’adda.
An gudanar da shari’ar ne a karkashin jagorancin Birgediya Janar Ugochukwu Unachukwu a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.
Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, shugaban kotun sojin ne ya bayyana hukuncin daurin Rai-da-rai ga Raphael Ameh, Ejiga Musa, da kuma Patrick Ocheje, biyo bayan samunsu da laifin aikata zargin da aka yi musu.
A ɓangaren hukuncin Omitoye Rufus, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp