Za a gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai na kasar Sin daga gobe Asabar 5 zuwa 10 ga watan Nuwanban wannan shekara.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, yayin bikin budewar CIIE da ya gudana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta bude kofa ga kasashen ketare, da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da kokarin mai da ci gaban kasar damar raya tattalin arzikin duniya.
A matsayinsa na bikin baje kolin kasa da kasa na farko a duniya, mai taken shigo da kayayyaki, bikin na CIIE ya kasance wani muhimmin dandali na saye da sayarwa na kasa da kasa, da inganta zuba jari da musaya tsakanin al’ummomi da na al’adu, da hadin gwiwar dake shafar kowa da kowa tun lokacin da aka fara gudanar da shi a shekarar 2018.
A yayin bukukuwan CIIE guda 4 da aka gudanar a baya, yawan darajar kwangilolin da aka kulla ta kai dalar Amurka biliyan 272.3. (Ibrahim/Bello)