Yau Asabar, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da tawagar kasar dake hukumar UNESCO, wato hukumar kyautata ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, sun gudanar da “bikin nuna fina-finan kasar Sin” a hedikwatar hukumar, inda aka gabatar da ra’ayin kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da yadda kasar Sin take kokarin zamanantar da kanta.
Wannan shi ne karo na farko da aka nuna fina-finai sama da 50 a “bikin nuna fina-finan kasar Sin” a wata kungiyar kasa da kasa.
Shugaban CMG, Mista Shen Haixiong ya gabatar da jawabin dake cewa, a shekara ta 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a hedikwatar hukumar UNESCO, inda ya nuna cewa, ya dace mu koyi hikimomi da ilimomi daga mabambantan al’adu, don karfafa gwiwar dan Adam, da nuna musu goyon-baya a fannin tunani, a wani kokari na shawo kan kalubalolin dake addabar daukacin bil’adama.
Shen ya ce, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, zai hada gwiwa tare da abokai na gida da na waje, don kara gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, ta hanyar amfani da fina-finai, ta yadda za’a karfafa gwiwar duniyar mu baki daya, da samar da makoma mai haske ga daukacin al’umma. (Murtala Zhang)