Yau Lahadi 22 ga wata ne, aka yi bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta kasashen Asiya karo na 4, a babban filin wasa na Olympics dake birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin.
Kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta mutane masu bukata ta musamman ta kasashen Asiya, da kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya ta Hangzhou, sun gudanar da taron manema labarai a yau Lahadi 22 ga wata da yamma, inda suka bayyana cewa, an riga na shirya tsaf domin gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta mutane masu bukata ta musamman ta Asiya karo na 4 a birnin na Hangzhou.
- Tinubu Ya Sadaukar Da Kai Ga Manufofin Nijeriya Da Afrika A Duniya – Minista
- Abin Da Ya Sa Muka Sa Takin Zamani Cikin Tallafin Jama’a – Gwamnan Filato
Babban mai magana da yawun gasar ta bana, Chen Weiqiang ya bayyana cewa, gasar ta bana tana kunshe da manyan wasanni 22, hade da wasu kanana 564, wadda za ta samu halartar mutane kusan 5200 daga kasashe da yankuna 44, ciki har da ‘yan wasanni kusan 3100, da jami’an tawagogin kasa da kasa sama da 2090. Har ila yau, jami’an kula da fasahohi sama da 1550 da ‘yan jaridu fiye da 3090 su ma za su halarci gasar, abun da ya sa ta zama irinta mafi kasaita a tarihi.
Mista Chen ya kuma ce, an tanadi na’urori da kayayyaki na musamman da dama, a wani kokari na hidimtawa mahalarta masu bukata ta musamman, da samar musu da tabbaci don su halarci gasar yadda ya kamata.
Rahotannin sun kuma ruwaito cewa, tawagar kasar Sin na kunshe da mutane 723 a bana, ciki har da ‘yan wasanni 439, wadanda za su halarci dukkan manyan wasanni 22, da wasu kananan guda 397. (Murtala Zhang)