Yayin da gasar wasannin kasa da kasa ta shekarar 2025 ke karatowa, an gudanar da bikin karba, da kaddamar da fitilar gasar a Asabar din nan, a shahararren gidan adana kayan tarihi na Sanxingdui, dake birnin Chengdu na kasar Sin.
Kaddamar da fitilar gasar a yau, ya alamta fara kidayar kwanaki 12, gabanin bude gasar karo na 12, wadda za ta gudana tsakanin ranakun 7 zuwa 17 ga watan Agusta dake tafe. An tsara kewayawa da fitilar tsawon kilomita 11, a yankunan biranen Chengdu, da Deyang, da Meishan, kuma mutane 120 za su yi karba-karbar kewayawa da ita, wanda hakan ke alamta ruhin gasar da kyakkyawan zumuncin da take kullawa.
An ayyana ‘yar wasan motsa jiki Huang Zhangjiayang daga birnin Chengdu, wadda ta taimakawa kasar Sin lashe lambar zinari a wasan nuna fasahohin lankwasa jiki yayin gasar Olympics ta lokacin zafi a birnin Paris, a shekarar bara, a matsayin wadda za ta fara zagayawa da fitilar. Yayin da kwararren dan wasan kwallon tebur na kasar Sin Ma Long, zai kasance na karshe da zai kewaya da fitilar. An baiwa Ma Long wannan dama ne bisa kwarewarsa, da kuma nasarori masu yawa da ya cimma, a gasannin da ya wakilci kasar Sin a cikinsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp