Naira ta samu tagomashi a kasuwar musayar kudade da kuma a kasuwar bayan fage, inda aka yi hada-hadar sayar da ita, kan Naira 1,500 har ta haura Dala, da aka yi hada-hadar ta kan Dala 1.
Hakan ya biyo bayan kokarin da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi ne, na tabbatar da darajar ta Naira, inda a kauswannin biyu, aka yi musayar Naira ne, kan Naira 562 ako wacce Dala daya.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Sin Na Maraba Da Jarin Kasa Da Kasa A Fannin Kamfanonin Fasaha
Naira ta dai samu wannan nasarar ce, hada-hadar kasuwancinta da aka yi a ranar 21 ga watan Fabirairun 2025.
Wasu alkaluma da Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar a hukumace sun suna cewa, an rufe hada-hadar a kasuwannin biyu, a ranar 21 ga watan Fabirairun 2025, inda aka sayar da Naira kan Naira 1,500 sabanin Dala, da aka sayar kan Dala 1.
Kazalika, haka a kasuwar bayan fage, an yi hada-hadar kasuwancin Naira inda kan, 500 sabanin Dala da aka samu Dala 1 wanda hakan ya nuna sabanin yadda aka yi hada-harta a baya kan Naira 1510, inda kuma aka yi hada-hadar Dala, kan Dala 1.
Bugu da kari,a kasuwar an yi hada-hadar Naira kan 1,960, inda kuma Fam na kasar Birtaniya, ya fadi, wanda aka sayar kan Fam 1, sabanin a kwana daya da aka sayar da Naira kan 1,950 aka kuma sayar da Fam kan, Fam 1.
Hakazalika, Dalar Kanada, ta yi asara a kasuwar, inda aka sayar da Naira kan 1,200, aka kuma sayar da ta kan CA1, sabanin yadda a kwana daya aka sayar da Naira kan 1,150, aka kuma sayar da CA kan CA1.
An yi hada-hadar Naira, kan Naira 5, sabanin takardar Euro da aka yi hada-hadarta kan Naira 1,590, inda takardar ta Euro aka sayar da ita, kan Euro 1, sabanin kwana daya baya, da aka sayar da Naira kan 1,595 aka kuma sayar da Euro, kan Euro 1.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp