An raba jadawalin yadda za’a fafata wasannin cin kofin duniya na mata inda Nijeriya tana rukuni na biyu da ya hada da Australia da Jamhuriyar Ireland da Canada a gasar ta mata a 2023 da za a yi a Australia da New Zealand.
Wannan shi ne karon farko da Jamhuriyar Ireland za ta buga gasar, tana kuma rukuni tare da wadda ta lashe Olympic wato Canada, sai Ingila wadda ta lashe gasar nahiyar Turai za ta fafata da Denmark da China a rukuni na hudu tare da ko dai Senegal ko Haiti ko kuma Chile.
- Kasar Sin Ta Jinjinawa Hanyoyin Da Kasashen Yankin Manyan Tafkunan Afirka Ke Bi Wajen Magance Matsalolinsu
- Bai Kamata A Sabawa Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Ba
Za a fara wasan daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga watan Agustan shekara ta 2023 kuma za a yi bikin bude gasar a Auckland, New Zealand, sannan a yi bikin rufe wasannin a Australia a birnin Sydney.
Tawagogi 32 ne za su kece raini, kenan an samu kari daga 24 da suka kara a Faransa a gasar kofin duniya a 2019 kuma cikin tawagogi 32, biyar daga ciki za su buga gasar kofin duniya a karon farko da suka hada da Morocco da Philippines, da Jamhuriyar Ireland da Bietnam da kuma Zambia.
Ga yadda jadawalin yake:
Group A: New Zealand, Norway, Philippines, Switzerland.
GroupB: Australia, Republic of Ireland, Nigeria, Canada.
Group C: Spain, Costa Rica, Zambia, Japan.
Group D: England, wadda ta ci wasan cike gurbi a rukunin B, Denmark, China
Group E: USA, Bietnam, Netherlands, Wadda ta ci cike gurbi a rukunin A.
Group F: France, Jamaica, Brazil, Wadda ta ci cike gurbi a rukunin C.
Group G: Sweden, South Africa, Italy, Argentina
Group H: Germany, Morocco, Colombia, Korea Republic.