An yi jana’izar mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji (Dakta) Yunusa Muhammad Danyaya, (OON) a Ningi da ke jihar Bauchi a yau Lahadi inda dubban jama’a suka yi alhini da jimamin rashinsa.
Mai martaba Danyaya wanda ya kasance Sarki na biyu mafi daɗewa a ƙaragar mulki a tarihin jihar Bauchi, ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi biyo bayan rashin lafiya da ta riske shi a wani asibiti da ke Kano.
- PDP Ta Lashe Zaɓen Shugabanin Ƙananan Hukumomin Bauchi Gaba Ɗaya
- Mutane 5 Sun Rasu Dalilin Ruwa Kamar Da Bakin Ƙwarya A Bauchi
Marigayin dai ya kwashe shekaru 46 a matsayin Sarkin Ningi, ya rasu ya na da shekaru 88 a duniya, ya kuma bar mata huɗu da ‘ya’ya 24 gami da jikoki.
Da ya ke magana bayan jana’izar, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin uwa, jigo wanda ya kasance jagoran koyi bisa irin kyawawan abubuwan da ya gudanar a yayin da ke mulki, kana da irin gudunmawar da ya bayar wajen daurewar zaman lafiya, haɗin kai da cigaban masarautar Ningi, jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah ya sanya shi cikin Aljanna maɗaukakiya tare da cewa za su jima su na tuna kyawawa halayyarsa.
A binciken da Wakilinmu ya gudanar ya gano cewa shi dai Ɗanyaya ya zama sarkin Ningi ne a shekarar 1978 inda kuma aka ɗaukala lifafarsa zuwa sarki mai daraja ta ɗaya a shekarar 1998.
An haifi Alhaji Yunusa a shekarar 1936 a garin Ningi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp