Alkaluma sun nuna cewa, an yi tafiye-tafiyen da suka shafi shiga da fita daga kasar Sin kimanin miliyan 16.34, yayin hutun kwanaki takwas na bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka, wanda ya kare a jiya Laraba.
A cewar hukumar kula da shige da ficen, matsakaicin adadin tafiye-tafiyen da aka yi a kowace rana ya zarce miliyan 2, inda aka samu karuwa kaso 11.5 kan mizanin shekara-shekara.
Yayin hutun, adadin tafiye-tafiyen da baki suka yi zuwa kasar Sin ya zarce kaso 21.6 zuwa miliyan 1.43. Jimilar baki dubu 751 ne suka shigo kasar, karuwar kaso 19.8, ciki har da dubu 535 da suka shigo karkashin shirin soki visa, inda adadin ya karu da kaso 46.8 a mizanin shekara-shekara. (Fa’iza Mustapha)