Daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Nuwamba ne, gidauniyar kare hakkin dan Adam ta kasar Sin da kwamitin kasa kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, suka gudanar da taron karawa juna sani kan harkokin shari’a da kare hakkin dan Adam karo na 12 tsakanin Sin da Amurka ta kafar bidiyo.
Masana da shehunan malamai sama da 30 daga fannonin da abin shafa na kasashen Sin da Amurka ne suka halarci taron, inda aka gudanar da mu’amala mai zurfi kan batutuwan da suka shafi masana’antu, da kasuwanci, da kare hakkin dan-Adam.
A shekarar 2009 ne, aka kafa taron karawa juna sani na tsakanin kasashen Sin da Amurka kan harkokin shari’a da kare hakkin dan Adam, kuma muhimmin dandali ne da aka tsara don musanyar jama’a da tattaunawa tsakanin kasashen biyu. Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu kan batutuwan da suka shafi harkokin shari’a da kare hakkin dan Adam, da karfafa zumuncin tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Ibrahim)