A Zamfara, hukumomin kula da yaƙi da cutar shan-inna sun bayyana cewa an yi wa yara fiye da miliyan biyu rigakafin cututtukan mashaƙo da sankaran yara a faɗin jihar, yayin da sama da miliyan 1.8 na yara ‘yan ƙasa da watanni 59 suka karbi rigakafin cutar shan-inna.
Jami’in kula da Cibiyar Gaggawar Polio ta Jihar Zamfara, Dekta Murtala Salahudeen, ya bayyana hakan a Gusau a ranar Asabar yayin taron manema labarai na bikin Ranar Polio ta Duniya.
- Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
- Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda
Ya ce, wannan nasara babbar alama ce ta ci gaba, musamman wajen kare rayukan yara daga cututtukan da ke kashe mutane amma ana iya kauce musu da rigakafi.
A cewar Salahudeen, Ranar Yaƙi da Cutar Polio ta Duniya muhimmiyar dama ce ta faɗakar da jama’a kan barazanar da cutar shan-inna ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki, tare da sake duba nasarori da kalubalen da ake fuskanta.
Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin bunkasa lafiya — musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) — ya taimaka matuƙa wajen cimma wannan gagarumar nasara.
“Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta-baci a bangaren lafiya, kuma hakan ya zame ginshiqin da ya taimaka wajen samun tallafi, goyon baya da isassun ma’aikata don tabbatar da an kai rigakafi ko’ina,” inji shi.
Dekta Salahudeen ya kara da cewa WHO, UNICEF, Chigari, Sultan Foundation da Salina Foundation sun taka rawar gani wajen taimakawa jihar ta isa ga dukkan al’ummomi, ciki har da yankunan da ke da wahalar kaiwa.
Ya ce, waɗannan ƙungiyoyi sun samar da tallafin kudi, kayan aiki, horo ga ma’aikatan lafiya, da kuma goyon baya wajen aiwatar da rigakafi a kananan hukumomi 14 na jihar.
Daga cikin manyan nasarorin da aka samu, a cewar shi, akwai damar kai rigakafi har ma zuwa yankunan Fulani makiyaya da wuraren da ake gani a matsayin “hard-to-reach”, baya ga tallafin jami’an tsaro da ya taimaka wajen baje kolin ayyukan rigakafi cikin kwanciyar hankali.
“An samu damar ziyarar dukkan yankuna, har da na noma da kiwo, inda muka ga cewa ba zai yuwu mu bar kowane yaro a baya ba,” inji Salahudeen.
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada karfi da kungiyoyin hadaka, domin tabbatar da kawar da shan-inna baki daya, tare da cigaba da karfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin rigakafi.
 
			




 
							








