Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sha kashi a hannun abokiyar karawarta ta West Ham United a wasan da suka buga na gasar Carabao Cup a ranar Laraba.
Arsenal ta yi rashin nasara a hannun West Ham United da ci 3-1 bayan da kocin Arsenal Mikel Arteta ya ajiye manyan ‘yan wasansa a benci.
- Ku Yi Aiki Tukuru Ko Na Kore Ku, Tinubu Ga Ministoci
- Yaya Za A Cimma “Tsaro tare”? Dandalin Xiangshan Ya Gabatar Da Wasu Tunani
Kwallaye daga Muhammad Kudus da Jarrod Bowen sai kuma wadda Ben White ya ci gida su ne suka bai wa West Ham nasara a hannun Arsenal.
Duk da kwallo daya da kyaftin din Arsenal Martin Ordeegard ya jefa dab da za a tashi daga wasan, ba ta isa Arsenal ta wuce mataki na gaba ba.