An yi zama mai taken “kare hakkokin ‘yan kananan kabilu a sabon zamanin da muke ciki” a jiya Jumma’a 24 ga wata a fadar Palais des Nations dake birnin Geneva na kasar Switzerland, zaman da ya kasance wani bangare na taro na 52, na kwamitin hakkokin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya.
Kungiyar kula da mu’amalar harkokin kananan kalibu tsakanin kasar Sin da kasashen waje ce ta karbi bakuncin zaman, wanda ya samu halartar masana da kwararrun Sin da na kasa da kasa da dama.
Wani masani dan kabilar Uygur daga kasar Sin, mai suna Zunun Naser al-Din, ya yi bayani kan yadda kasarsa take kokarin tabbatar da hakkin ‘yan kananan kabilunta wajen samun ilimi, inda ya bayyana labarin kansa, game da yadda ya yi karatu cikin yaren Uygur tun lokacin yarintar sa, da yadda ya halarci jarrabawar neman shiga jami’a cikin yaren Uygur, da kammala karatun digiri na uku a fannin nazarin harshen Uygur, har ma da yadda yake gudanar da ayyukan nazari, gami da koyarwa a fannin yarukan kananan kabilu, da halartar ayyukan kiyaye yaruka, gami da al’adun gargajiya na kananan kabilun kasar.
A nasa bangare kuwa, mamban kungiyar kiyayewa, gami da raya al’adun jihar Tibet ta kasar Sin, Li Xi, ya bayyana yadda kasar sa take kokarin tabbatar da cewa, ‘ya’yan manoma da makiyaya, dake zaune a yankuna masu nisa sun samu damar zuwa makaranta. (Murtala Zhang)