Jam’iyyar APC ta lashe zabukan shugabannin kananan hukumomi da kansiloli 312 a daukacin kananan hukumomi 27 na jihar Borno.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yar takarar jam’iyyar APC a karamar hukumar Jere ta jihar, Inna Galadima, ta zama zababbiyar shugabar karamar hukumar, wacce ta zama mace ta farko da aka zaba shugabar karamar hukuma a jihar.
Inna Galadima, wacce ta taba zama kwamishina kuma mai ba da shawara ta musamman, jami’in zabe na karamar hukumar Jere, Farfesa Mohammed Konto ne ya bayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp